Hon. Sani Usman Naya na Gundumar Timdore a Karamar Hukumar Ganye ya taya wasu fitattun shugabanni da suka taka rawa a rayuwarsa da ci gaban al’umma murnar bikin Sallah.
A sakonsa na gaisuwar Sallah, Hon. Naya ya taya Mai Martaba Gangwari Ganye, Hakimin Ganye Alhaji Ahmed Nwangubi, Fasto Habila Istifanus, da Hakimin Garum murna da fatan alheri. Ya bayyana su a matsayin manyan mutane da suka taka rawar gani a rayuwarsa.
Har ila yau, ya aika da fatan alheri na Barka da Sallah ga al’ummar Gundumar Timdore, daukacin Karamar Hukumar Ganye, da kuma jama’ar Jihar Adamawa baki ɗaya, yana addu’ar zaman lafiya da cigaba.
Hon. Naya ya kuma yi kira ga manoma da su rungumi amfani da iri na zamani domin samun girbi cikin lokaci da samun albarka. Ya ce, “Da ikon Allah, yin hakan zai kawo sauki da inganci a harkar noma.”
A wani bangare na sakonsa, ya bukaci matasa da su rika goyon bayan juna tare da kawar da sabani, rashin jituwa da banbancin siyasa ko addini. “Hadin kai da zaman lafiya tsakanin mabambantan ra’ayoyi da addinai shi ne ginshikin cigaban kowacce al’umma,” in ji shi.
Bugu da ƙari, Hon. Naya ya yabawa Hakimin Timdore, Alhaji Idiris Sa’ad Gisilanbe bisa kasancewa jagora nagari kuma abin koyi ga jama’a.
Sakon Hon. Sani Usman Naya ya bayyana irin jajircewarsa wajen ganin an samu ci gaba mai dorewa a fannoni daban-daban na rayuwa a cikin al’umma, musamman a fannin noma, zaman lafiya da haɗin kai.
Rahoto daga Yirensuso Anthony Bakari
Ubangijin Allah ya biya ka, Allah ya kara bude hanya.